Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Wani rahoto na shafin labarai na Isra'ila "Walla" ya ce wannan yanki ya kai fiye da kadada miliyan biyu kuma yana tsakanin Masar da Sudan, kuma ya fi tudun Golan girma da kusan murabba'in kilomita 200. Kuma duk da cewa yana da albarkatu da kabilun makiyaya, amma kasashen biyu da ke makwabtaka da shi sun yi watsi da shi gaba daya, a cewar iƙirarinsa.
Rahoton shafin na Ibrananci ya kara da cewa, wannan yanki da ba shi da tituna masu kyau, otal-otal da hanyoyin sadarwa ta wayar hannu, a zahiri yana da aiki a ƙasa inda kabilar Ababda ta makiyaya ke zama tun zamanin daular Roma, kuma ana samun bunƙasar harkar haƙar zinare ta hanyar ma'aikata masu zaman kansu da manyan injuna, tare da sansanonin ma'aikata, kananan shaguna, masu canjin kuɗi, har ma da makiyaya masu dauke da makamai da ke kare yankin.
Rahoton na Ibrananci ya yi nuni da cewa, dalilin wannan yanayi na rashin daidaituwa shi ne tsarin mulkin mallaka na Birtaniya. A shekara ta 1899, Birtaniya ta zana iyaka madaidaiciya tsakanin Masar da Sudan, sannan ta canza ra'ayinta a shekara ta 1902 ta zana wani layi mai karkata wanda zai kiyaye motsin kabilu ba tare da bayyana iyakokin hukuma ba. Bayan samun 'yancin kai na kasashen biyu, rikici ya ɓarke a kan yankin Halayib mai albarka da ke daura da teku. Masar ta tsaya kan layin farko wanda ke mallaka ma ta Halayib, yayin da Sudan ta tsaya kan layi na biyu wanda ke mallaka mata yankin. Dangane da dokar kasa da kasa, neman Bir Tawil yana nufin yin watsi da Halayib kai tsaye, wanda ya haifar da matsananciyar diflomasiyya wanda ya kai ga barin yankin a matsayin sakakai.
Walla ta ce wannan rashin ikon mulki ya jawo hankulan wasu mutane masu ban mamaki, inda mutane tara suka yi ƙoƙarin shelanta kansu a matsayin masu mulkin yankin, mafi shaharansu shi ne manomi ɗan Amurka Jeremiah Heaton wanda ya dasa tuta a can a shekara ta 2014 kuma ya kafa Masarautar Arewacin Sudan don cika burin 'yarsa ta zama gimbiya. Amma dattawan kabilun yankin sun dauki hakan a matsayin cin mutunci kuma sun yi masa barazanar cutar da shi idan ya dawo, suna kin yarda su kasance ƙarƙashin mulkin da ba na gaske ba ta hanyar intanet.
Jaridar Ibrananci ta kara da cewa, jami'in diflomasiyya da marubuci ɗan Amurka Grant Arthur Gochan ya buga wata makala a jaridar "Times of Israel" inda ya gabatar da wani mafita mai sauyi, yana mai nuni da cewa Bir Tawil ya dace da wani ma'auni mai wuyar gaske na rashin ikon mallaka ko 'yan ƙasa na hukuma ko iƙirarin wata ƙasa ta uku, don haka za a iya mayar da wannan yanki zuwa wata ƙasa ta Falasdinu mai cikakken 'yancin kai.
Times of Israel ya yi nuni da cewa, shirin da aka tsara yana buƙatar amincewar Masar da Sudan tare da wasu manyan abubuwan ƙarfafa tattalin arziki da zuba jari daga kasashen yankin tekun Farisa, kuma zai fara da gina abubuwan more rayuwa na ruwan sha mai daɗi da hasken rana mai kimanin dala biliyan 80, wanda shine daidai da kuɗin sake gina Gaza. Manufar ita ce a mayar da kuɗin da ake batarwa a cikin kufan da aka lalata da sake gina shi akai-akai zuwa gina wata ƙasa ta zamani daga farko.
Jaridar Isra'ila "Maariv" ta ce wannan matakin zai kasance na son rai gaba daya, kuma za a bai wa Falasdinawa cikakken zama yan ƙasa, diyya ta kuɗi, da taimako wajen ƙaura ba tare da wani tilas ba. Za a sa sabuwar ƙasa ta kasance ba ta da makamai gaba daya, kuma za a sa ido da sojojin duniya irin na da ke cikin Sinai, kuma za a haramta samun ƙungiyoyin mayaka da ke dauke da makamai. Ta na mai ganin cewa wannan shiri ba mafita ce ta gaggawa ba, a'a, tsarin aiki ne da ke ba da madadin ga tashin hankali mara iyaka.
Ya kamata a tuna cewa yankin Bir Tawil yana arewa maso gabashin Afirka tsakanin Masar da Sudan, kuma yanki ya kai kimanin murabba'in kilomita 2060. Ana ɗaukarsa a matsayin daya daga cikin 'yan ƙasashe kaɗan a duniya da ba su ƙarƙashin ikon kowace ƙasa saboda sabani a cikin iyakokin da Birtaniya ta zana a shekarun 1899 da 1902.
Duk da tsananin yanayin hamada, yankin yana da ayyukan ɗan adam da haƙar zinare, kuma lokaci-lokaci ana samun shirye-shiryen diflomasiyya da ba a saba ba don amfani da rashi na ikon mallakarsa wajen magance rikice-rikicen yanki, wanda ke nuna hadaddun yanayin geopolitical na iyakokin da aka zana a zamanin mulkin mallaka.
..............
Your Comment